Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeAl'aduJihar Kogi na bincike kan basaraken daya ki tarbar Buhari

Jihar Kogi na bincike kan basaraken daya ki tarbar Buhari

Date:

Gwamnatin jihar Kogi ta tuhumi mai sarautar gargajiya ta Ohinoyi of Ebiraland, Dr Ado Ibrahim bisa zargin cin zarafin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamna Yahaya Bello.

 

An tuhumi basaraken da kauracewa tarbar Buhari yayin ziyarar sa jihar kogi a ranar 29 ga watan December 2022.

 

Wannan na kunshe cikin sakon da ma’aikatar kananan hukumomi da masarautun gargajiya ta aikewa basaraken dauke da sa hannun darektan alamuran masarautu Enimola Eniola.

 

Takardar ta bukaci Dr Ado Ibrahim ya rubuta wasikar kare kanshi daga zargin da ake masa kasa da awanni 48 da samun sakon ma’aikatar.

 

Hakazalika, an bukaci basaraken ya gurfana a gaban kwamitin binciken da gwamnatin jihar ta kafa domin kare kansa daga zargin cin zarafi da isgilin da rashin fitowarsa tarar tawagar shugaban kasar ya nuna.

 

Wata majiya daga masarautar ta bayyanawa manema labarai cewa sakon ya isa gareshi kuma kawo yanzu sarkin bai kai ga tsaida matakin da zai dauka ba nan gaba.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...