Mataimakin Gwamnan Kano Murtala Sule Garo, ya ce ƙofarsa a buɗe take domin karɓar shawarwari masu amfani wadada za su taimaka wajen ci gaban jihar a koda yaushe.
Garo ya bayyana hakan ne yayin da shugabannin ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah, JIBWIS, reshen Jihar Kano suka kai masa ziyara.
Sule Garo ya kuma nuna farin cikinsa bisa yadda ƙungiyar ta JIBWIS ta yaba da matakin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dauka ware sama da kujeru ashirin na aikin Hajjin bana ga mambobin kungiyar ta Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah.
Tun da farko a jawabin sa, Shugaban JIBWIS na Kano, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, ya ce sun kai ziyarar ne domin taya Mataimakin Gwamnan murnar sabon muƙamin na sa, inda Garo a matsayin shugaba mai biyayya, jajircewa da kyawawan halayen da ya kamata a yi koyi da su.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya Haka Pakistan na buƙatar Mataimakin Gwamnan ds ya isar da godiyar ƙungiyar ta su ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa baiwa JIBWIS kujeru 27 na aikin Hajjin bana.
