Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da hade Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta jihar zuwa ma’aikata guda daya.
Sabuwar ma’aikatar wadda za’a dinga kiranta da sunan Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi, za ta hada ayyukan kula da albarkatun ruwa, kare muhalli da kuma magance illolin sauyin yanayi karkashin tsari guda.
Da yake sanar da sauyin da aka samu, Kwamishinan ma’aikatar, Dr Dahiru Muhammad Hashim, ya godewa Gwamna Abba bisa amincewa da ya yi da shi wajen jagorantar sabuwar ma’aikatar.
Dr Dahiru ya ce matakin ya nuna kudirin gwamnatin Kano na inganta tsarin gudanarwa tare da kara hadin kai tsakanin bangarorin da ke da alaka da juna.
Ya kuma amince da cewa hade ma’aikatun biyu na tattare da kalubale, sai dai ya tabbatarwa da al’ummar Kank cewa an dauki matakan da suka dace domin tabbatar da sauyin ya gudana cikin nasara ba tare da tangarda ba.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Dr Hashim na bayyana cewa sabuwar ma’aikatar za ta gudanar da ayyukanta ne bisa manufofin ci gaban gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, musamman wajen magance matsalolin muhalli da fadada samar da ingantaccen ruwa mai dorewa ga al’ummar Kano.
