Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ta bai wa kamfanonin da ke gudanar da ayyukan gyaran da inganta hanyoyin samar da ruwa wa’adin watanni takwas kacal domin kammala ayyukansu, a wani yunkuri na cika alkawarin magance matsalar karancin ruwan famfo a fadin jihar kafin karshen wa’adin mulkin gwamnatin yanzu a shekarar 2027.
Mai rikon mukamin Kwamishinan Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Jihar Kano, Injiniya Dahiru M. Hashim, ne ya bayyana hakan yayin da yake ziyarar duba ci gaban aikin farfado da babban tankin ajiyar ruwa na Goron Dutse da ke Kano.
Kwamshinan ya ce gwamnati ta himmatu wajen tabbatar da samar da wadataccen ruwa mai tsafta ga al’ummar Kano, a don haka ne ta gindayawa ’yan kwangilar wa’adin da za su tabbatar da kammala ayyukan cikin lokaci.
A cewarsa, aikin gyaran tankin Goron Dutse na daga cikin muhimman ayyukan da gwamnati ke aiwatarwa domin kara karfin ajiyar ruwa da inganta rabon ruwa zuwa unguwanni daban-daban na birnin Kano da kewaye.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Kwamishina Dahiru Hashim na jaddada cewa gwamnati ba za ta amince da jinkiri ba, wanda hakan ce ta sanya ake yana sa’ido sosai kan yadda ayyukan ke gudana domin tabbatar da an samu sakamakon da ake bukata.
