Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKasuwanciJami’ar Amurka ta fitar da takardun karatun Tinubu

Jami’ar Amurka ta fitar da takardun karatun Tinubu

Date:

Jamiar jihar Chicago ta tabbatar da cewa shugaba Bola Tinubu halastaccen dalibin jamiar ne, inda ya kammala karatu a jamiar a 1979.

Wata sanarwa da jamiar ta fitar biyo bayan umarnin wata kotun birnin illinois da ta umarci jamiar ta fitar da bayanan ga dan takarar shugaban kasa na jamiyyar PDP a zaben 2023 Atiku Abubakar.

Jamiar tace Tinubun ya karanta sha’anin kasuwanci ne, amma ta dage cewa bata ajiye kwafin sakamakon diploma da take baiwa daliban ta.

Sai dai tace bayan dogon bincike ta iya gano wasu daga cikin sakamokon daliban, amma ba zata iya bayyana sunayen sub a saboda, tsare sirrin su.

Sai dai ta tabbatar da cewa babu na shugaba Bola Tinubu cikin wadanda ta gano

Amma ta ga wasu sakamakon da suka yi kama da irin wanda Atiku ke zargin Tinubun ya mikawa hukumar zabe.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...