Jami’ar Exeter dake Birtaniya zata fara karatun Degree a bangaren tsafi da tsubbace tsubbace daga shekarar 2024.
Guda cikin jami’an makarantar da zai jagoranci darasin Farfesa Emily Selove ya ce za a fara karatun Degree na biyu a bangaren tsafi biyo bayan yawaitar masu nuna sha’awa a bangaren.
Jami’ar zata bada damar karantar tarihi da kuma tasirin tsafi a cikin al’umma a duniya.
Za a fara karatun ne a watan Satumba na shekarar 2024.
Kwararru a bangaren tarihi da adabi da ilimin falsafa da addini da sauran bangarori zasu nuna rawar da tsafi yake takawa a yammaci da gabashin duniya.
Za a bayar da darasin ne a kwalejin arabiya da nazarin addinin musulunci dake jami’ar.