Saurari premier Radio
25.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiJAMB ta riƙe sakamakon jarabawar dalibai 64,624 a bana

JAMB ta riƙe sakamakon jarabawar dalibai 64,624 a bana

Date:

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta kasa JAMB, ta rike sakamakon jarabwar dalibai 64,624 da suka rubuta jarabawar a bana.

Lokacin da yake sanar da sakin sakamakon jarabawar a yau Litinin, shugaban hukumar, Farfewa Ishaq Oleyede ya ce an rike sakamakon ne domin gudanar da bincike, saboda wasu dalilai.

Farfesa Oloyede ya kara da cewa duk da haka, hukumar ta saki sakamakon dalibai 1,842,464 daga cikin dalibai 1,904,189 da suka rubuta jarabwar ta UTME a tsawon kwanaki shida.

A cewarsa, kashi 0.4 daga wadanda suka rubuta jarabawar sun samu maki sama da 300, sannan kashi 24% suka samu maki akalla 200.

Sai dai ya ce, duk da haka dalibai 80,810 sun yi fashin rubuta jarabawar.

A cewarsa hukumar ta soke lasisin cibiyar rubuta jarabawar dake makarantar, Makama School of Technology, da ke Bichi a nan Kano saboda rashin yin aiki yadda ya kamata.

Latest stories

Related stories