Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana goyon bayansa ga matakin bai wa yankin Kudu tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, yana mai cewa hakan zai ƙara ƙarfafa haɗin kan ƙasa da adalci.
Kwankwaso ya bayyana matsayinsa ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X bayan babban taron ƙasa na jam’iyyar.
A cewarsa, bai wa yankin Kudu damar fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa na wa’adin shekaru huɗu kacal zai taimaka wajen inganta haɗin kai, daidaito da kuma daidaiton siyasa a Najeriya.
Tsohon gwamnan ya bayyana taron jam’iyyar a matsayin mai tarihi, yana yabawa mambobin jam’iyyar bisa nuna haɗin kai da jajircewa wajen kare dimokuraɗiyya.
Haka kuma ya yaba wa tsohon gwamnan Jihar Bayelsa kuma jagoran jam’iyyar NDC, Seriake Dickson, bisa shirya taron da ya bayyana a matsayin mai nasara da tasiri.
Kwankwaso ya kuma gode wa Peter Obi da mambobin tafiyar Obidient Movement bisa halartar taron da kuma bayar da gudunmawa wajen nasarar taron.
Ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa jam’iyyar za ta ci gaba da aiki domin dawo da fata, ƙarfafa haɗin kai, da gina kyakkyawar makoma ga yan Najeriya.
