Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da sabbin tsauraran matakai domin yaƙi da amfani da miyagun ƙwayoyi a makarantun sakandare, inda ta sanya gwajin ƙwaya ya zama dole ga ɗalibai.
Sabuwar dokar ta tanadi cewa duk sabon ɗalibin da zai shiga makarantar sakandare sai an yi masa gwajin miyagun ƙwayoyi kafin a ba shi gurbin karatu.
Haka kuma, ɗaliban da aka samu da amfani da ƙwayoyi za a riƙa kai su jinya da gyaran hali, sannan idan aka ci gaba da samun su da laifi bayan an yi musu gyara, makaranta na da ikon dakatar da su na wani lokaci.
Sabbin matakan na ƙunshe ne a cikin kundin ƙasa na yaƙi da amfani da miyagun ƙwayoyi a makarantu na Najeriya.
Takardar ta bayyana cewa manufar ita ce rage yawaitar amfani da miyagun ƙwayoyi tsakanin ɗalibai tare da samar da ingantaccen yanayin koyarwa da koyo a makarantu.
A cewar dokar, duk makarantu za su riƙa gudanar da gwajin ƙwaya lokaci-lokaci ko kuma ba tare da sanarwa ba a kalla sau ɗaya a kowace shekarar karatu.
An kuma haramta wa ɗalibai mallaka ko amfani da miyagun ƙwayoyi ba tare da amincewar hukumomin makaranta ba.
Gwamnatin ta ce za a gudanar da gwaje-gwajen ne tare da haɗin gwiwar cibiyoyin lafiya na gwamnati da aka amince da su a matakin jiha da tarayya.
