Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoHukumar Kare Hakkin Mai Saye ta Kama Buhunan Alkama Sama da 600...

Hukumar Kare Hakkin Mai Saye ta Kama Buhunan Alkama Sama da 600 a Kano

Date:

Umar Idris Shuaibu

Hukumar kare hakkin mai saye da mai sayarwa ta jihar Kano ta kama wata Alkama sama da buhu dari shida wadda ake zargin ba mai kyau ba ce.

 

Rahotanni na nuni da cewa an samu Alkamar ce a wani rumbun ajiyar kayayyaki a kwanar Tifa cikin unguwar Dawakin Dakata, dake karamar hukumar Nassarawa.

 

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran hukumar, Musbahu Aminu Yakasai ya fitar inda ya aikewa Premier Radio.

 

Da yake jawabi a madadin mai rikon shugabancin hukumar Dr. Baffa Babba Dan Agundi, babban mataimaki na musamman ga Gwamnan jihar Kano a hukumar Salisu Muhammad, ya bayyana cewa tuni aka kwashe alkamar aka kai ta rumbun ajiyar kayayyaki na hukumar don fadada bincike.

 

Ya kuma kara da cewa, an debi wani kaso na Alkamar a matsayin samfuri don yin gwaji akai, da hakan zai tabbatar da ingancinta ko kuma akasin hakan.

 

Salisu Muhammad ta cikin sanarwar na cewa, nasarar na zuwa ne bisa kokarin al’umma na baiwa hukumar bayanan sirri wanda daga bisani hukumar ta bincika kuma ta tabbatar.

Latest stories

Related stories