Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya umarci shugabannin hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen ceto dukkan mutanen da ke tsare a hannun masu garkuwa, tare da tabbatar da tsaro a faɗin ƙasar gabanin babban zaɓen 2027.
Ministan tsaro, janar Christopher Musa mai ritaya, ne ya bayyana hakan ranar Alhamis bayan wani taron majalisar tsaro ta ƙasa da shugaban ƙasar ya jagoranta a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Ministan ya ce shugaban ƙasar ya buƙaci jami’an tsaro da su gudanar da ayyukan da za su kai ga gano wuraren da ake ɓoye waɗanda aka yi garkuwa da su, tare da ceto su. Ya kuma umarce su da su ƙara matsa lamba kan ’yan ta’adda da ’yan bindiga, tare da wargaza sansanoninsu a duk inda suke a Najeriya.
Dangane da zaɓen 2027, Musa ya ce Tinubu ya jaddada cewa dole ne jami’an tsaro su kasance masu nuna adalci da rashin goyon bayan kowace jam’iyyar siyasa, domin bai wa dukkan ’yan takara da jam’iyyu damar shiga zaɓe cikin aminci.
Ya ƙara da cewa wajibi ne jami’an tsaro su kare ’yan Najeriya daga barazana ko tsoratarwa ta siyasa, domin su samu damar zaɓar shugabanninsu cikin kwanciyar hankali.
Ministan ya kuma buƙaci jama’a da su taimaka wa hukumomin tsaro ta hanyar kai rahoton duk wani abu da suka lura da shi da zai iya kawo barazana ga zaman lafiya, yana mai cewa za a ɗauki mataki kan duk jami’in tsaro da aka samu yana aikata ba daidai ba.
