Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce jam’iyyar za ta ɗauki duk matakan da suka dace domin rage farashin fetur idan ta samu nasarar lashe zaɓen 2027, ciki har da yiwuwar dawo da tallafin man fetur.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Channels ya yi da shi a cikin shirin Politics Today ranar Alhamis, 15 ga Oktoba, 2026. Ya ce farashin makamashi ya yi tsada matuƙa, kuma har yanzu ’yan Najeriya ba su farfaɗo daga matsin tattalin arzikin da cire tallafin man fetur ya haifar ba.
Ya ce shi da ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, da jagoran jam’iyyar, Seriake Dickson, sun tattauna batun, kuma sun cimma matsaya kan buƙatar rage farashin makamashi domin sauƙaƙa wa al’umma wahalhalun rayuwa.
Kwankwaso ya kuma bayyana cewa ya kamata a magance cin hanci da rashawa a masana’antar mai, yana mai cewa hakan na iya taimakawa wajen samar da mafita mai ɗorewa ga matsalar tsadar fetur.
Shugaba Tinubu ne ya sanar da cire tallafin man fetur a ranar 29 ga Mayu, 2023, a ranar da ya karɓi rantsuwar kama aiki. Matakin ya biyo bayan hauhawar farashin fetur da kuma ƙarin kuɗin sufuri da kayayyaki, lamarin da ya ƙara matsin rayuwa ga ’yan Najeriya.
Sai dai Kwankwaso bai bayyana takamaiman tsarin tallafin da NDC za ta yi amfani da shi ko yadda za ta samar da kuɗin aiwatar da shirin ba. Ya ce manufar jam’iyyar ita ce rage tsadar makamashi da inganta rayuwar jama’a idan ta samu mulki.
