Ma’aikatar ilimi ta tarayya ta sanar da cewa daga yanzu masu neman gurbin karatu a Kwalejojin Ilimi na Tarayya (Federal Colleges of Education) domin karatun NCE ba za su sake rubuta jarabawar UTME da JAMB ke shiryawa ba.
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a yayin taron tsara manufofi na shekarar 2026 da Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta JAMB ta gudanar a Abuja ranar Litinin.
A cewar ministan, matakin na daga cikin kokarin gwamnati na kara saukaka hanyoyin shiga manyan makarantu da kuma karfafa sha’awar dalibai wajen neman guraben karatu a fannin koyarwa.
Ya kara da cewa wannan sassauci ba zai takaita ga masu neman shiga kwasa-kwasan ilimi kawai ba, har ma ya shafi masu neman guraben karatu a fannonin fasaha, noma da sauran darussa masu alaka da su.
Sai dai ya bayyana cewa duk da cire sharadin rubuta UTME, dole ne masu neman guraben su mallaki cikakkun takardun kamala sakandire, kamar yadda doka ta tanada.
Haka kuma, ya ce har yanzu za su bi ta tsarin tantancewa na JAMB, domin tabbatar da sahihancin bayanansu da kuma gudanar da rajista yadda ya kamata.
Matakin na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da kokarin farfado da sha’awar shiga kwalejojin horas da malamai, yayin da gwamnati ke neman hanyoyin inganta bangaren ilimi da samar da karin kwararrun malamai a fadin kasar.
