Saurari premier Radio
37.8 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKasuwanciGwamnatin Tarayya na Kashe Biliyan 18.39 a Tallafin Man Fetur Kullum- Ministar...

Gwamnatin Tarayya na Kashe Biliyan 18.39 a Tallafin Man Fetur Kullum- Ministar Kudi

Date:

Hafsat Bello Bahara

Ministar kudi da tsare-tsare Zainab Shamsuna Ahmad tace ma’aikatar ta na biyan kamfanonin saida man fetur masu zaman kansu naira triliyan 6.219 na kudin tallafin man fetur tsakanin shekarar 2013 zuwa 2021.

Ta bayyana hakan ne yayin taron kwamitin binciken tallafin man fetur da majalisar wakilai ta kafa wadda Ibrahim Aliyu ke jagoranta.

Ministar kudin ta bayyana cewar gwamnatin tarayya a kullum tana kashe akalla biliyan 18.397 a tallafin man fetur din.

Ta bayyanawa kwamitin binciken cewar gwamnatin bazata iya cigaba da daukar nauyin tallafin man fetur din ba. Saboda Hakan tana me Bada shawarmar a kirawo taron masu ruwa da tsaki domin a samar da mafita.

Taron zai hada da Shugaban Majalissar dattijai, jam’iyun siyasar kasar nan da sauran wadanda abun ya shafa domin yanke hukunci akan cigaba ko barin tsarin tallafin man fetur din baki daya.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Manoman tumatir na kokawa kan mummunar asara

Manoman tumatir a jihar Katsina na kokawa kan yadda...