Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKasuwanciAlkaluman Hauhawar Farashin Kayayyaki a Najeriya ya kai Kokoluwa da ba a...

Alkaluman Hauhawar Farashin Kayayyaki a Najeriya ya kai Kokoluwa da ba a Taba Gani ba Cikin Shekaru 28.

Date:

Alkaluman hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya a duk shekara ya kai wata sabuwar kokoluwa da baa taba ganin ba cikin shekaru 28, wato kashi 33.95 cikin 100 a watan Mayu, kamar yadda hukumar kididdiga ta bayyana.

Wannan dai ya kara tsananta wahalhalun da al’umma ke ciki, abin da ake alakantawa da sauye-sauyen tattalin arziki na manufofin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Kungiyoyin Kwadago, wadanda suka dakatar da yajin aikin da suka kira neman a kara musu sabon mafi karancin albashi, sun yi zargin cewa sauye-sauyen na cutar da talakawa, tare da jefa miliyoyin mutane cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa a cikin shekaru da dama da suka gabata.

Hauhawar farashin kayan abinci, wanda ya haifar da mafi yawan tashin farashin kayayyaki a Najeriya, ya tashi zuwa kashi 40.66 cikin 100 daga kashi 40.53 cikin 100 a watan da ya gabata.

TRT

 

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...