Gwamnatin Kano ta yaba da rawar da kungiyoyin addini ke takawa a jihar wajen samar da zaman lafiyar da fahimtar juna a tsakanin mabiyan su a jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.
Mataimakin Gwamnan Kano Murtala Sule Garo ne ya bayyana hakan lokacin da ya karɓi baƙuncin Majalisar Shurar darikar Tijjaniyya da kungiyar darikar Ƙadiriyya a ofishinsa.
Yayin da yake karɓar tawagar Majalisar Shurar Tijjaniyya reshen Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Sheikh Sani Shehi Maihula, Mataimakin Gwamnan ya yaba da irin gudunmawar da ƙungiyar ke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da zaman jituwa a faɗin jihar.
Garo ya bayyana ziyarar ta su a matsayin ƙwarin gwiwar da za ta ƙara masa kuzari wajen gudanar da ayyukan ofishinsa cikin gaskiya, riƙon amana da sadaukarwa, tare da buƙatar ƙarin addu’o’i domin samun nasarar abubuwan da gwamnatin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, da zaman lafiya da ci gaban Kano da Najeriya baki ɗaya.
Tun da farko, shugaban Majalisar Shurar Tijjaniyya, Sheikh Sani Shehi Mai Hula,ya bayyana cewa majalisar tana da wakilai a dukkan ƙananan hukumomi 44 na Kano, yana mai cewa majalisar za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulkinta tare da bayar da shawarwari masu amfani domin ci gaban jihar.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa Mataimakin Gwamnan ya kuma karɓi tawagar Ƙungiyar Ƙadiriyya ƙarƙashin jagorancin Sheikh Karibullah Nasir Kabara, wadda Alkali Ahmad Zaruk Kabara ya wakilta, inda a jawabin Zaruk ys tabbatarwa da Mataimakin gwamnan cewa shugabannin Ƙadiriyya a shirye suke su ci gaba da bayar da shawarwari da goyon baya domin samar da ci gaba mai ɗorewa a Kano.
