Gwamnatin Kano ta ce ta farfado da kamfanin sarrafa Shara ya zuwa taki mallakin ta, da nufin sanya jihar a sahun kasashen duniya wajen sarrafa sharar zuwa abubuwa masu amfani ga al’umma.
Shugaban hukumar kwashe shara ta Kano Dr Muhammad S Khalil ne ya bayyana hakan, inda ya ce kamfanin wanda yake a unguwar Dorayi tuni ya fara samar da takin na zamani ta hanyar sarrafa sharar.
A cewar Dr Khalil gwamnatin Kano ta aike da takin dakin gwaji tare da gudanar da gwaje-gwaje akan ingancin sa, inda kuma tuni masana suka tabbatar da nagartar sa wanda hakan ya bawa gwamnati damar mayar da hankali gafan-gadan a bangaren tattalin sharar tare da buɗe kofa ga masu zuba jari daga ciki da wajen Najeriya.
Dr Khalil ya ce gwamna Abba Kabir Yusuf ya wadata hukumar da dukkan kayan aikin da take bukata da inganta walwalar ma’aikatan hukumar ta hanyar ninka alwasu din su da gyara motoci da siyan sabbi domin aiki da kuma samar da asibiti a cikin hukumar domin kula da lafiyar ma’aikatan ta.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Dr Khalil na cewa hukuma ta kuma samar da kwandon zuba shara akan titunan Kano da cikin babura masu kafa 3 domin tabbatar da zaunar da Kano cikin tsafta.
