Gwamnatin Kano ta jaddada aniyarta na ci gaba da baiwa ɓangaren ilimi fifiko tare da haɗa kai da Gwamnatin tarayya da ma sauran ƙungiyoyi.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan yayin da karamar Ministar Ilimi ta kasa Suwaiba Sa’id Ahmed ta kai masa ziyara a gidan gwamnatin Kano.
Gwamnan ya ce shirin AGILE ya zama wata babbar kafa ta inganta ilimi musamman ta fuskar gine-ginen makarantu da inganta malamai.
Tun da farko a jawabin ta, karamar Ministar Ilimi Farfesa Suwaiba Sa’id Ahmed, ta sanar da Gwamnan cewa jihar Kano ta samu amincewar bankin duniya kan gina sabbin makarantu 49 da za su lashe sama da naira biliyan 23, inda ta ce tuni aka baiwa ‘yan kwangila kudin fara aikin.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Ministar na cewa samar da makarantun zai taimaka wajen fadada damar samun ilimi ga al’ummomin da ke da ƙarancin makarantu, tare da yabawa Gwamnatin Kano bisa samar da ingantattun ayyukan gine-ginen makarantu da ta gani yayin ziyarar ta.
