Gwamnatin Jihar Kebbi ta zargi tsohon Ministan Shari’a na Najeriya, Abubakar Malami, da amfani da matsalar rashin tsaro da halin da waɗanda hare-haren ƴan bindiga suka shafa ke ciki domin samun goyon bayan siyasa gabanin zaɓen 2027.
A wata sanarwa da mai ba Gwamna Nasir Idris shawara kan harkokin sadarwa da dabaru, Yahaya Sarki, ya fitar, gwamnatin ta zargi Malami da jam’iyyar ADC da amfani da ziyarar sansanonin ƴan gudun hijira wajen neman farin jini.
Gwamnatin ta ce tana ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro da kayan aiki, tare da ɗaukar matakan taimaka wa al’ummomin da hare-haren ƴan bindiga suka shafa.
Sai dai wani mataimaki ga Malami ya yi watsi da zarge-zargen, yana mai cewa gwamnatin jihar na nuna fargabar ƙarfin adawar da suke mata.
Ya ce za su mayar da martani kan zarge-zargen a lokacin da ya dace.
