Hukumar jin dadin Alhazai ta Jjhar Jigawa ta ƙaddamar da kwamitin tattarawa, nazari da tantance bayanan maniyyata aikin Hajjin shekarar 2027, domin tabbatar da ingantaccen shiri da gudanar da aikin cikin tsari.
Da yake ƙaddamar da kwamitin, Shugaban hukumar, Alhaji Ahamed Umar Labbo, ya jaddada muhimmancin tattara bayanai sahihai da tantance su, musamman yayin da ake shirin fara aikin bayar da biza ga maniyyata.
Labbo ya bayyana cewa kwamitin zai kasance ƙarƙashin jagorancin Daraktan Ayyuka na hukumar, Mohammed Garba, tare da Daraktan Gudanarwa da Kuɗi, Mohammed Umar Sambo, da Babban Akanta, Muntari Mohammed.
Kwamitin ya kuma ƙunshi shugabannin shiyyoyin hukumar da mataimakansu a faɗin jihar ta Jigawa.
Shugaban ya ce kawo yanzu, hukumar ta kammala kusan kashi 40 cikin 100 na shirye-shiryen aikin Hajjin 2027, tare da buƙatar mambobin kwamitin su gudanar da aikinsu cikin ƙwazo da gaskiya.
Ya kuma sanar da cewa nan ba da jimawa ba za’a fitar da jadawalin wayar da kai da horas da maniyyata a shiyyoyi da ƙananan hukumomi 27 na jihar.
