Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa Adamu Aliyu, mai shekara 22, da Mubarak Abdulsalam, mai shekara 20, hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samunsu da laifin kashe maigidansu, Dahiru Musa, mai shekara 32.
Kotun ta kuma yanke wa Sadiq Sunusi, mai shekara 19, hukuncin ɗaurin shekara bakwai a gidan yari, bisa samunsa da laifin taimakawa wajen ƙona gawar mamacin domin ɓoye laifin.
Mai shari’a Fatima Adamu ta bayyana cewa masu gabatar da ƙara sun tabbatar da laifukan da ake tuhumar matasan da su ba tare da wata tantama ba.
Lauyan gwamnati, Salisu Muhammad-Tahir, ya shaida wa kotun cewa lamarin ya faru ne a ranar 29 ga Satumba, 2024, a unguwar Gaida Ƴan Kusa da ke Kano.
Ya ce matasan biyu sun kashe Dahiru Musa ta hanyar ba shi gubar kashe beraye, sannan suka daba masa wuƙa sau da dama.
A cewarsa, washegari an yi amfani da fetur wajen ƙona gawar mamacin a wani gini da ba a kammala ba.
Masu gabatar da ƙara sun gabatar da shaidu biyar da wasu hujjoji a gaban kotun, yayin da waɗanda ake tuhumar suka musanta zarge-zargen.
Kotun ta bai wa waɗanda aka yanke wa hukuncin wa’adin kwanaki 90 domin ɗaukaka ƙara idan ba su gamsu da hukuncin ba.
