Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya karɓi mutane 163 da jami’an tsaro suka ceto daga hannun masu garkuwa da mutane a jihar.
An miƙa mutanen ga gwamnatin jihar ne a Ilorin ranar Juma’a, bayan nasarar aikin ceto da jami’an tsaro suka gudanar.
Gwamnan ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da jami’an tsaro bisa nasarar kubutar da mutanen, tare da bayyana godiyarsa ga jami’an tsaron da suka haɗa kai wajen gudanar da aikin.
Rahotanni sun ce an yi garkuwa da mutanen ne a ranar 3 ga Fabrairu, lokacin da ’yan bindiga suka kai hare-hare a garuruwan Woro da Nuku da wasu ƙauyukan da ke jihar.
Hare-haren sun yi sanadin mutuwar aƙalla mutane 75, yayin da wasu da dama suka tsere daga gidajensu.
Rahotanni sun kuma kiyasta cewa kusan mutane 170, galibi mata da yara, aka yi garkuwa da su a lokacin hare-haren.
Gwamnatin Jihar Kwara ta sanar da sakin mutanen ranar Laraba, kafin daga bisani a miƙa su a hukumance ga gwamnatin jihar a Ilorin.
