Gwamnatin Kano ta yi bikin rabawa matasa 521, wadanda suka fito daga gundumomi 10 na karamar Hukumar Gwale takardar daukar aikin gwamnati.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Karamar Hukumar Gwale, Alhaji Abubakar Mu’azu Mojo, ya ce shirin daukar ma’aikatan wata alama ce ta kudirin Gwamna Abba Kabir Yusuf na karfafa matasa, inganta shugabanci ga kowa da bunkasa rayuwar al’umma.
Mojo ya ce an zabo wadanda suka ci gajiyar shirin ne daga cikin matasan da suka taka rawa a shirye-shiryen gwamnati da na al’umma, domin ba su damar samun abin dogaro da kai tare da tallafawa iyalansu.
Mojo ya ce za’a tura sabbin ma’aikatan zuwa sassa da dama na karamar hukumar wadanda suka hada da fannin ilimi, lafiya da rundunar tsaro ta Neighbourhood Watch domin taimakawa wajen inganta ayyukan gwamnati da ci gaban al’umma.
Shi ma da yake nasa jawabin, Kwamishinan Makamashi na Kano, Alhaji Gaddafi Shehu, ya bayyana bikin a matsayin wani babban ci gaba ga wadanda suka samu aikin, yana mai cewa hakan na nuna yadda gwamnatin Gwamna Yusuf ke fifita bukatun jama’a, tare da bukatar sabbin ma’aikatan da su kasance jakadu nagari da bayar da gudunmawa wajen cigaban Kano.
