Watanni 8 tun bayan da gwamnatin tarayya hadin gwiwa da gwamnatin Kano suka ƙaddamar da aikin titin Wuju-Wuju, har yanzu ba’a fara aiwatar da aikin ba, lamarin da ya jefa al’ummomin yankunan da abin ya shafa cikin damuwa da fargaba.
Titin wanda ake sa ran zai taimaka wajen sauƙaƙa zirga-zirga tare da rage matsalolin ambaliya a yankunan da abun ya shafa, an ƙaddamar da aikin sa tun a wata Satumbar 2025, ya ci gaba da kasance cikin mawuyacin hali tun bayan ƙaddamar da aikin, ba tare da ganin jami’ai sun fara gudanar da aiki ko kawo kayan aiki wurin ba.
Sai dai faduwar damunar bana ya ƙara jefa mazauna yankunan cikin zulumi, yayin da suke fargabar yadda ruwan sama ke ci gaba da zama barazana ga rayukansu da dukiyoyinsu, la’akari da yadda hanyoyi kan cika da ruwa tare da haddasa matsaloli ga zirga-zirga.
Idan za’a iya tunawa bayan ƙaddamar da aikin a wancen lokaci Premier Radio ta kawo muku rahoto na musamman inda ta tattauna da mazauna yankin da aikin ya shafa.