Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yaba wa shugabannin ƙasa na kungiyar manoma ta kasa bisa jajircewarsu wajen kare muradan manoma da bunƙasa harkokin noma a jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa na ba da muhimmanci ga noma a matsayin ginshiƙin tattalin arzikin jihar, yana mai jaddada cewa ci gaban ɓangaren zai taimaka wajen samar da wadataccen abinci da inganta rayuwar al’umma.
Buni ya kuma yi alƙawarin ƙara ƙarfafa matakan tsaro da inganta walwalar manoma, domin su samu damar gudanar da ayyukansu cikin kwanciyar hankali ba tare da fargabar hare-hare ko wasu barazanar tsaro ba.
Ya ce gwamnati za ta ci gaba da haɗin gwiwa da ƙungiyoyin manoma da sauran masu ruwa da tsaki wajen samar da tallafi, kayan aikin gona da sauran abubuwan da za su taimaka wajen haɓaka noman amfanin gona da kiwo.
Gwamnan ya jaddada cewa inganta tsaro da samar da yanayin da ya dace da harkokin noma na da matuƙar muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arzikin karkara da kuma tabbatar da wadatar abinci a Yobe.
A nasa ɓangaren, shugabannin AFAN sun nuna jin daɗinsu kan yadda gwamnatin jihar ke kulawa da manoma, tare da bayyana aniyarsu ta ci gaba da bayar da gudunmawa wajen bunƙasa harkokin noma da samar da abinci a jihar.
