
Aminu Abdullahi Ibrahim
Al’ummar karamar hukumar Tudun Wada sun bukaci gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya karasa musu titin Five- Kilometer.
A cewar mutanen yankin dakatar da aikin da gwamnati tayi na barazana ga muhalli da lafiyar al’umma.
Wani mazaunin karamar hukumar Buhari Yusuf ya ce a duk lokacin da ruwan damuna ya dauka sun fuskantar barazana musamman mata masu ciki.

”Muna rokon gwamna ya kawo mana dauki ya ceto rayuwar mata masu ciki dake fuskantar kalubale sanadiyar rashin kammala aikin titinmu”, a cewar sa.
Shazali Garba, ya ce sun sha yin korafi amma har yanzu gwamna bai waiwaiye su ba.
Ya ce rashin kammala aikin zai iya sawa su kaurece kada kuri’a.
Fatima Aminu ta ce matsalar titin na Five kilometer na barazana ga yara ‘yan makaranta.
Ta roki gwamna Abba Kabir Yusuf da ‘Yan majalisar yankin da shugabancin karamar hukumar su gaggauta karasa aikin titin.
