Saurari premier Radio
32.9 C
Kano
Thursday, April 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGhana ta koro yan Najeriya 16 gida

Ghana ta koro yan Najeriya 16 gida

Date:

Hukumar kula da shige da fice ta Kasa (NIS) a ranar Juma’a ta ce an kori ‘yan Najeriya 16 daga kasar Ghana bisa zargin su da aikata laifuka ta shafukan intanet.

 

Dokta Chukwu Emeka, Konturola na rundunar ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a garin Seme na jihar Legas.

 

 

Dakta Chukwu Emeka ya ce“Hukumar kula da harkokin kudi da leken asiri ta Ghana ta zargi su da aikata laifuka ta yanar gizo amma daga binciken farko da muka yi, mun gano cewa wasu daga cikinsu an rude su zuwa ga aikata laifin saboda tsantsar son zuciya da burin yin arziki dare daya da ya addabi matasan yanzu”

 

Dakta Emeka ya kara da cewar “Abin takaici ne yanda Yan Najeriya ke bulaguro zuwa kasashen waje da sunan neman kudi kuma ba su sami ainihin abin da suka je neman a Ghana ba.”

 

 

Binciken da aka yi ya kuma nuna cewa mafi yawansu sun bar kasar ne ta hanyoyin da ba su dace ba ko kuma ta cikin teku zuwa wasu kasashen yammacin Afirka,” inji shi.

 

 

Kwantrolan ya bukaci ‘yan Najeriya da su rika tafiya da ingantattun takardu, tare da yin abun da ya dace kamar yadda dokar kasar da suka je ta tanada.

Latest stories

Hukumar EFCC ta musalta zargin da ake mata na fara bincikar tsohon Gwamnan kogi.

Shugaban hukumar EFCC mai hukunta masu yiwa tattalin arziki...

Majalisar dokokin Kano ta nemi a dakatar da KEDCO kan yanke wuta.

Majalisar Dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar data...

Related stories

Hukumar EFCC ta musalta zargin da ake mata na fara bincikar tsohon Gwamnan kogi.

Shugaban hukumar EFCC mai hukunta masu yiwa tattalin arziki...

Majalisar dokokin Kano ta nemi a dakatar da KEDCO kan yanke wuta.

Majalisar Dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar data...