Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Friday, April 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKotu bata wanke Nnamdi Kanu ba-Ministan shari'a

Kotu bata wanke Nnamdi Kanu ba-Ministan shari’a

Date:

Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya ce kotu ba ta wanke shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, daga zarge-zargen ta’addanci ba.

 

Ministan ya ce Gwamnatin Tarayya na nazarin hukuncin kotun daukaka kara da ta sallami Kanu, duk da cewa yana fuskantar zargin ta’addnaci.

 

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran ministan Umar Jibrila Gwandu ya fitar ranar Juma’a.

 

Sanarwar ta ce domin kawar da shakku kotun da ta salami Kanu bata wanke shi daga dukkan tuhume tuhumen da ake yi masa baSaboda haka.

 

“Hukumomin da suka dace za su bi matakan Shari’a da suka dace kan tuhumar, wanda nan gaba za a sanar da jama’a.

 

“Umarnin sallamar da kotun ta bayar a kan abu daya ne, wato dawo da shi Najeriya a asirce daga kasar waje.

 

“Jama’a su sani cewa sauran batutuwa da ake zargin sa a kansu gabanin tiso keyarsa zuwa Najeriya a asirce bayan ya tsallake beli na nan da ingancinsu, kotu za ta yanke hukunci a kai.”

 

Hakan kuwa na zuwa ne bayan lauyan shugaban na IPOB, Maxwell Okpara, ya ce wajibi ne Gwamnatin Tarayya ta saki Nnamdi Kanu a cikin kana 30 daga rana da kotun ta yanke hukuncin, idan har gwamnatin ba ta daukaka kara ba.

 

A cewarsa, bangarensu zai mika wa bangaren gwamnati takardar hukuncin domin yin abin da ya dace, na sakin wanda yake karewa ko kuma daukaka kara.

 

Sai dai Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya ce, “Gwamnati za ta yi amfani da duk damar da doka ta bayar game da umarni wannan kotu na sakinsa kan yadda aka dawo da shi Najeriya.

 

Latest stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...

Related stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...