Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYanzu-yanzu:ASUU ta janye yajin aiki na wucin gadi

Yanzu-yanzu:ASUU ta janye yajin aiki na wucin gadi

Date:

Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) ta janye yajin aikin da ta shafe wata takwas tana gudanarwa.

 

Kungiyar ASUU ta amince ta janye yajin aikin ne a babban taronta na Majalisar Zartarwa da ya gudana a Abuja, wanda shugabannin rassanta da sauran manyan jami’ai suka halarta.

 

A safiyar Juma’a, wani babban jami’in ASUU da ya halarci taron ya  ce, “Gaskiya ne, mun janye yajin aikin… Nan gaba da safiyar nan Shugaban ASUU na Kasa zai fitar da sanarwa a hukumance,” kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

 

Janye yajin aikin ASUU na zuwa ne wata takwas cif ke bayan malaman jami’o’in gwamnati a fadin Najeriya sun bi umarnin uwar kungiyar na daina aiki daga ranar 14 ga watan Fabrairu, 2022.

Latest stories

Related stories