33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiEl-Rufa'i ya caccaki gwamnatin tarayya

El-Rufa’i ya caccaki gwamnatin tarayya

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya ce gwamnatin tarayya ta gaza a bangaren mai da kuma iskar gas, inda ya ce ya kamata ta fice daga bangaren kasuwancin.

El-Rufai ya bayyana hakan ne yayin taron zuba jari da hukumar karfafa zuba jari ta jihar Kaduna ta shirya.

Gwamnan ya ce bangarori da ke aiki a wannan kasa kamar bangaren nishadi da harkar sadarwa da kuma fasaha da sauransu, gwamnati ba ta da hannu a cikinsu.

A cewarsa, babu wani abu da ya sauya tun bayan cefanar da babban kamfanin man fetur na Najeriya a watan Yulin 2022.

Ya kara da cewa duk da irin kokari da shugaban kamfanin na NNPC, Mele Kyari yake yi, kamfanin ya gaza a bangaren kasuwancin mai.

“NNPC babbar matsala ce ga Najeriya wacce ta fi karfin mutum daya wanda muddin ba a shawo kan matsalar ba, to za ta iya durkusar da Najeriya,” in ji El-Rufai.

Latest stories