Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBuhari ne zai fadi lokacin fara yakin neman zaben  Tinubu

Buhari ne zai fadi lokacin fara yakin neman zaben  Tinubu

Date:

Jam’iyyar APC  ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari  ne zai yanke hukunci kan lokacin da za a fara yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar.

Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasar Mr Festus Keyamo ne ya bayyana haka bayan kammala taron da shugabannin jam’iyyar suka gudanar tare da gwamnoni da kuma kwamitin yakin neman zaben  a ranar Laraba a Abuja.

Jam’iyyar dai ta yi ta sake ranakun game da ranar kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasar, sakamakon rikice-rikice da suka dabaibaye  jam’iyyar  da mutanen da ke cikin kwamitin yakin neman zaben.

Keyamo  ya kuma kara da cewa  kawunan ƴaƴan jam’iyyar a hade suke kuma jam’iyyar suce zata samu nasarra a babban zaben da zaa gudanar a shekara mai zuwa.

Latest stories

Related stories