Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBuhari ya  rantsar da sabon Alkalin Alkalai na kasa

Buhari ya  rantsar da sabon Alkalin Alkalai na kasa

Date:

A yau larabar nan shugaban kasar nan Muhammadu Buhari ya rantsar da sabon  Alkalin Alkalan kasar nan  Mai Shari’a Olukayode Ariwoola a babban birnin taryya Abuja.

Wannan na zuwa ne bayan da ya shafe watanni hudu yana rikon kwarya biyo bayan murabus din da Mai shari’a Ibrahim Tanko yayi.

A wani sako da fadar shugaban kasar ta wallafa a shafin Tuwita ya nuna cewa Alkalin Alkalan Najeriyar ya karbi  rantsuwar fara aikin  ne da safiyar yau Laraba.

An haife Mai Shari’a Olukayode Ariwoola a watan Agustan shekarar 1954 a Jihar Oyo, kuma ya yi alkalanci a Kotun Daukaka Kara ta kasar nan, kafin ya samu karin matsayi zuwa Kotun Koli.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories