24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiSojoji sun kashe Ali Dogo da wasu mutum 30

Sojoji sun kashe Ali Dogo da wasu mutum 30

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Sojojin Saman Najeriya sun samu nasarar kashe kasurgumin dan fashin dajin nan da ya addabi Jihar Kaduna, Ali Dogo, tare da wasu mutanensa 30.

Rahotanni sun ce sojojin ‘Operation WHIRL Punch’ sun fattaki Dogo, wanda aka fi sani da Yellow da mayakansa ne a karshen makon da ya gabata.

Sojojin sun yi wa Yellow da mayakan nasa dirar mikiya ne a daidai lokacin da suke tsaka da tattaunawa a gidan Alhaji Gwarzo, inda jirgin yakin ya sakar wa ginin wuta ya hallaka su baki daya.

Kazalika, sojojin sun sake kai samame kan ‘yan bindiga a yankin Mando da ke Arewa maso Yammacin Kaduna.

Bayanai sun ce sojoji sun kai samamen ne bayan tattara bayanan sirrin da suka samu game da shirin ‘yan bindigar da kuma inda suke.

An ji mai magana da yawun rundunar sojojin sama, AC Edward Gabkwet, ya tabbatar da nasarorin da suka samu.

Haka nan, ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da fatattakar ‘yan ta’adda da harkokinsu a shiyyar Arewa maso Yamma.

Latest stories