Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta ƙasa (NARD) ta yi barazanar shiga yajin aiki na sai baba-ta-gani daga ranar 10 ga watan Agusta, idan har gwamnatin tarayya ta gaza cika buƙatun da ta gabatar.
Ƙungiyar ta ce matakin ya biyo bayan abin da ta bayyana a matsayin gazawar gwamnati wajen aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma a baya, musamman waɗanda suka shafi biyan bashin albashi, inganta walwalar likitoci da kuma kyautata yanayin aiki.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, matsayar ta fito ne a ƙarshen taron Kwamitin Zartarwarta, wanda aka gudanar a jihar Gombe daga ranar 26 zuwa 31 ga watan Yuli.
A yayin taron, wakilan ƙungiyar sun yi nazari kan yadda aka aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma da gwamnatin tarayya, tare da duba matsalolin da ke ci gaba da addabar fannin lafiya a Najeriya.
Da yake jawabi bayan taron, shugaban NARD, Dakta Mohammad Usman Suleiman, ya bayyana rashin gamsuwar ƙungiyar kan jinkirin da gwamnati ke yi wajen cika alƙawuran da aka ɗauka, duk da tattaunawar da aka shafe watanni ana gudanarwa.
Ya ce ƙungiyar ta tsawaita wa’adin fara yajin aiki har sau huɗu domin bai wa gwamnati damar warware matsalolin, amma har yanzu mafi yawan buƙatunta ba su samu biyan bukata ba.
