
Ishaq Sani Dambazau
Majalisar Ɗinkin Duniya ce ta ware ranar 7 ga watan Yuli a matsayin Ranar Kiswahili ta Duniya, domin nuna muhimmancin harshen Kiswahili wajen bunƙasa ilimi, al’adu da haɗin kai tsakanin al’ummomi.
An fara ware wannan rana ne bayan Hukumar Ilimi da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta UNESCO ta amince da ita a shekarar 2021, kafin daga bisani Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya ya tabbatar da bikin a matakin duniya.
Kiswahili na daga cikin harsunan Afirka da suka fi yawan masu magana, inda ake kiyasin sama da mutum miliyan 200 ke amfani da shi a matsayin harshen uwa ko kuma harshen sadarwa a ƙasashe da dama na Gabashi, Tsakiya da Kudancin Afirka.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa bikin na bana na da nufin ƙarfafa amfani da harsunan Afirka a fannonin ilimi, bincike, fasaha da ci gaban zamantakewa, tare da nuna irin gudunmawar da Kiswahili ke bayarwa wajen ƙarfafa haɗin kai da fahimtar juna tsakanin al’ummomi.
Har ila yau, Majalisar ta jaddada cewa kare da bunƙasa harsuna na daga cikin hanyoyin tabbatar da al’adu da tarihin al’umma, tare da ba wa kowane harshe damar taka rawa wajen cimma manufofin ci gaba mai ɗorewa a duniya.
