Sama da mahajjata miliyan 1.5 daga ƙasashen waje ne suka isa Ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin bana, adadin da ya zarce na shekarar 2025, duk da tashe-tashen hankulan da ake fuskanta a yankin Gabas ta Tsakiya.
Wani jami’in gwamnatin Saudiyya ya tabbatar cewa sama da miliyan 1.5 na mahajjata daga ƙasashe daban-daban sun riga sun shiga ƙasar domin halartar ibadar Hajji ta wannan shekara.
Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da rikicin da ya biyo bayan hare-haren da aka ce Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran a ƙarshen watan Fabrairu ya ƙara tayar da hankali a yankin, inda Iran ta mayar da martani da jerin hare-hare kan wasu wurare a Saudiyya da ƙasashen yankin Gulf.
Wannan lamari ya haifar da tangardar zirga-zirgar jiragen sama tare da ƙarin kuɗin tafiye-tafiye.
Rahotanni sun bayyana cewa manyan kamfanonin jiragen sama a ƙasashen Hadaddiyar Daular Larabawa, Qatar da Bahrain sun yi ƙoƙarin dawo da ayyukansu yadda ya kamata bayan makwanni na rushewar jadawalin jirage da kuma soke tashi a wasu lokuta.
Duk da waɗannan ƙalubale, mahajjata na ci gaba da tururuwa zuwa Saudiyya domin cika wannan muhimmin aikin ibada.
Ana sa ran adadin mahajjatan zai ƙaru a cikin kwanaki biyu masu zuwa yayin da ake ci gaba da karɓar baƙin daga sassa daban-daban na duniya, kafin fara manyan ayyukan Hajji a ranar Litinin.
A shekarar da ta gabata, jimillar mahajjata da suka gudanar da aikin Hajji sun kai 1,673,320, ciki har da 1,506,576 daga wajen Saudiyya.
Hajji na ɗaya daga cikin rukunan Musulunci guda biyar, kuma wajibi ne ga duk Musulmi mai hali ya gudanar da shi aƙalla sau ɗaya a rayuwarsa.
