Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) da ta gaggauta komawa kotu domin neman janye umarnin da ya haifar da rufe asusun bankunan gwamnatin jihar Osun.
A cewar shugaban, ɗaukar irin wannan mataki a wannan lokaci bai dace ba, yana mai cewa muhimmancin tabbatar da adalci tare da kauce wa duk wani abin da ka iya haifar da zargin son rai.
Tinubu ya bayyana cewa babban dalilin tsoma bakinsa shi ne yadda zaɓen gwamnan jihar Osun ke gabatowa, wanda aka shirya gudanarwa a ranar 15 ga watan Agusta. Ya ce ci gaba da rufe asusun gwamnatin jihar na iya kawo cikas ga gudanar da harkokin gwamnati da kuma shafar shirye-shiryen zaɓen.
Tun da farko, EFCC ta rufe asusun gwamnatin jihar Osun ne bayan samun umarnin kotu a ranar 5 ga watan Agusta.
Sai dai Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya yi Allah-wadai da matakin, inda ya zargi hukumar da yunƙurin siyasantar da lamarin tare da kawo cikas ga biyan albashin ma’aikata da gudanar da ayyukan gwamnati.
Shugaba Tinubu ya sake jaddada cewa gwamnatinsa na ci gaba da goyon bayan yaƙi da cin hanci da rashawa, amma ya buƙaci hukumomin da ke aiwatar da doka su riƙa yin la’akari da maslahar jama’a da kuma dacewar lokacin ɗaukar irin waɗannan matakai.
Umarnin shugaban na nufin EFCC za ta bi hanyoyin shari’a domin neman a buɗe asusun bankunan gwamnatin jihar Osun.
