
Aminu Abdullahi Ibrahim
Hukumar EFCC, ta sake buɗe bincike kan zarge-zargen da suka shafi tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku Abubakar, bayan tsohon ɗan majalisar wakilai, Ehiozuwa Johnson Agbonayinma, ya shigar da ƙorafi yana neman a gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin aikata laifukan kuɗi.
Ƙorafin na neman a dawo da batun da ya samo asali tun shekarar 2006, tare da roƙon hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta sake duba binciken da aka gudanar a lokacin da Malam Nuhu Ribadu ke shugabantar EFCC, da kuma nazarin wani rahoto da wani ƙaramin kwamitin Majalisar Dattawan Amurka ya fitar daga baya.
Da yake magana kan lamarin, Agbonayinma ya ce EFCC ta tabbatar masa da karɓar ƙorafinsa, wanda aka rubuta a ranar 27 ga Agusta, 2026, sannan aka karɓa a hukumance a ranar 1 ga Satumba, 2026.
An shigar da ƙorafin ne ta hannun lauyansa, Cif Hannibal Egbe Uwaifo, SAN. A cikin ƙorafin, ya nemi hukumar ta sake duba rahoton binciken da ta fitar a baya, tare da ɗaukar matakin da ya dace kan zarge-zargen.
Tsohon ɗan majalisar ya je hedikwatar EFCC da ke Jabi, Abuja, inda ya amince da ƙorafin a hukumance tare da amsa tambayoyin masu bincike.
Agbonayinma ya ce bai kamata a bar batun ya ci gaba da zama ba tare da an warware shi ba.
A cikin ƙorafin, Agbonayinma ya bukaci EFCC ta sake duba rahotonta na Satumba 2006 kan Atiku, tare da wani rahoto da ƙaramin kwamitin binciken dindindin na Majalisar Dattawan Amurka ya fitar a ranar 4 ga Fabrairu, 2010. Ya ce ya kamata a yi amfani da waɗannan takardu wajen tantance matakin da ya dace a ɗauka.
Ƙorafin ya yi zargin cewa a baya EFCC ta nuna cewa za a iya gurfanar da Atiku bayan ya bar mukamin mataimakin shugaban ƙasa.
Agbonayinma ya bayyana abin da ya kira rashin ɗaukar mataki a matsayin sakaci wajen gudanar da aikin hukuma. Ya kuma ce sake bin diddigin lamarin zai nuna ko hukumar tana da niyyar tabbatar da cewa manyan mutane masu tasiri a siyasa ma suna fuskantar bincike bisa doka.
Ya kuma bayyana cewa ya shigar da ƙorafi ga shugaban Amurka, Donald Trump, dangane da zarge-zargen.
A lokacin da aka wallafa rahoton, kakakin EFCC, Dele Oyewale, bai riga ya mayar da martani ga saƙonnin da aka aika masa domin samun sabon bayani kan binciken ba.
