Kwalejin nazarin ilimin addinin musulunci da shari’a wato LEGAL ta yi Alla…. wadai da wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ya zargi mahukuntan kwalejin da yunƙurin soke yin karatu a fannin Alqur’ani da hadisi, da kuma hana mata sanya Niqabi a cikin makarantar.
Da yake karin bayani kan lamarin, daraktan hulɗa da jama’a na kwalejin Dr Salisu marafa Sagagi, ya ce zargin bashi da tushe balle makama.
A cewar marafa, kwalejin bata hana kowa shiga cikin ta da Niqab ba, sai dai dole ne kowace ɗaliba ta buɗe fuskarta tare da nuna ID card ga jami’an tsaro domin su tabbatar da cewa ɗalibar kwalejin ce kafin a bata damar shiga, domin tabbatar da tsaro da ingantuwar tarbiyya.
Kwalejin ta kuma bayyana takaicin ta kan batun soke karatu a fannin alqur’ani da hadisi wanda ta ce sune ginshiƙin samar da ita, inda Marafa yace yanzu haka kwalejin tayi nisa wajen ɗaga darajar fannin daga professional diploma ya zuwa diploma ta ƙasa da matakin digiri.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Dr Marafa na yin kira ga al’ummar Kano da su yi watsi da duk wasu zarge-zarge da marasa kishin kano da neman tayar da fitina domin biyan bukatar kan su suke yunƙurin kunnawa don tabbatar da zaman lafiya da ci gaban ilimi a faɗin jihar.
