![]()
Hukumar EFCC, na shirin gurfanar da shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo, a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan wasu zarge-zargen da suka haɗa da halasta kuɗaɗen haram da kuma bayar da tallafin ta’addanci.
A cewar takardun tuhumar da EFCC ta shigar a kotu, hukumar na zargin Bodejo da karɓa da kuma mallakar wasu kuɗaɗe da suka kai kusan dala miliyan 2 da dubu dari biyar da talatin, waɗanda ake zargin sun samo asali ne daga haramtattun ayyuka.
Tuhumar ta ƙunshi laifuka 12.
EFCC ta kuma yi zargin cewa a watan Janairun shekarar 2022, Bodejo ya karɓi dala dubu dari biyu a tsabar kuɗi daga wata majiya da hukumar ke zargin tana da alaƙa da ayyukan da suka saɓa wa dokokin hana halasta kuɗaɗen haram.
Lamarin na zuwa ne bayan wasu shari’o’i da bincike da hukumomi suka gudanar kan zargin alaƙar wasu mutane da cibiyoyi da ayyukan tallafa wa ta’addanci da kuma safarar kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Bello Bodejo bai ce komai kan zarge zargen ba.
Ana sa ran kotu za ta fara sauraron shari’ar bayan gurfanar da shi.
