Saurari premier Radio
37.8 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDalibai zasu sake rubuta jarabawar Jamb ta shekarar 2022

Dalibai zasu sake rubuta jarabawar Jamb ta shekarar 2022

Date:

Aminu Abdullahi Ibrahim

 

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta kasa (JAMB) ta sanya ranar 6 ga watan Augusta amatsayin ranar da daliban da suka samu matsala wajen rubuta jarabawar ta shekarar 2022 zasu sake rubutawa.

 

Jamb ta sanar da hakanne a rahoton mako mako da take fitarwa ta hannun mai magana da yawunta Fabian Benjamin, a ranar Litinin.

 

Yace an sanya ranar ne ga wadanda suka samu matsala wajen rubuta jarabawar a baya.

 

Yajin aikin ASUU: Dalibai na zanga-zanga a Kano

 

Ta ce bayan tantancewa da masu ruwa da tsaki da kwararru na hukumar sukayi kan wadanda suka samu matsala wajen rubuta jarabawar hakan tasa ta amince da sanya musu ranar 6 ga watan na Agusta domin sake rubutawa.

 

Hukumar ta Jamb ta kara da cewa bayan nazartar cibiyoyin rubutar jarabawar guda goma a jahohi biyar na kasar nan tare da gano cewa an shirya magudin jarabawar a guraren hakan tasa ta soke jarabawar da daliban cibiyoyin suka rubuta.

 

Ta kuma ce dukkan daliban da suka fuskanci matsala a cibiyoyin zasu sake rubuta jarabawar.

 

Sai dai hukumar ta Jamb ta ce sake rubuta jarabawar bai shafi wadanda suka ki zuwa rubuta jarabawar ba a baya.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...