33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiBa zamu iya kawo karshen matsalar harkokin jirgin sama a kasar nan...

Ba zamu iya kawo karshen matsalar harkokin jirgin sama a kasar nan ba-Hadi Sirika

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Mukhtar Yahya Usman

Ministan sufurin jiragen sama na kasa Hadi Sirika, ya ce za a ba za a iya kowa karshen matsalolin da harkar sufurin jiragen sama ke fuskantaa kasar nan ba.

Hadi Sirika ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da kugiyar masu harkar sufuri a kasar nan.

Ya ce matsalalolin da bangaren sufurin jiragen sama ke fuskanta a kasar nan, sun sha kan ma’aikatarsa.

Ya ce wannan ba matsala ce da za a kawo karshenta cikin kankanin lokaci ba, saboda matsala ce ta duniya baki daya, ba Najeriya kadai ba.

Matsalar makamashi matsala ce da ta addabi duniya baki daya.

“A cewarsa yanzu haka akwai matsalar tsadar man jirgi a kasashe kama daga Amurka har zuwa New Zealand.

“Amma matsalar ta fi kamari a Najeriya saboda ba ma sarrafa shi a kasarmu, sannan ga tashin farashin Dala” In ji Ministan

Latest stories