Daga Hafsat Bello Bahara
Masana tattalin arzikin kasa sun ce akwai yiwuwar gwamnati mai kamawa ta gaza yin kasafin kudi.
Wannan jawabin ya biyo bayan rahoton rubu’in farko na tattalin arzikin kasa da ministar kudi Zainab Ahmad ta fitar da ya nuna adadin ruwan bashin da kasar ke fitarwa ya wuce kudin shigar ta da naira biliyan 300.
Rahoton ya nuna cewa a halin yanzu adadin kudin shigar kasa tsakanin watan Junairu da watan Yuni naira tiriliyon 1.63 ne yayin da adadin kudin bashin da kasar take biya akan basukan da ake binta tiriliyon 1.94.
Da yake tsokaci kan batun, Farfesa Kabiru Isah Dandago, na sashen tsimi da tanadi a jami’ar Bayero, ya ce wannan lamarin yana haska cewar matsin rayuwa da tsananin talauci zai karu a fadin kasar nan.
Farfesa Dandago, ya ce akwai bukatar yan kasa su farga su kuma binciki ‘yan takara masu burin darewa shugabanci kan tsare-tsaren da suka fitar domin magance wannan matsalar.
Za’a fara amfani da kudin bai daya na (ECO) a kasashen afurka.
Manazarci kan harkar siyasa Dr Murtala Muhammad, na jami’ar kimiya dake Wudil ya ce kasashen da su ka cigaba na yin amfani da bashi su bautar da kasashe masu tasowa kamar Nigeria wanda babban tarnaki ne ga tsarin domokradiyar kasar.
Wani hasashe da asusun bada lamuni na duniya ya fitar a farkon shekarar nan ya alamta cewa Nigeria zata dinga biyan naira 92 akan dukkan naira darin da aka kashe wajen yin hidimar kasa.