Bello Turji, ya fito ya yi magana bayan harin da ya yi sanadin mutuwar wasu sojoji a jihar Sokoto.
A baya dai Daily Trust ta ruwaito cewa aƙalla sojoji biyu sun rasa rayukansu yayin da wasu suka samu raunuka sakamakon fashewar wani bam da aka dasa a hanya (IED) a kan motar sojoji da ke kan hanyarsu ta zuwa ƙauyen Bargaja da ke ƙaramar hukumar Isa ta jihar Sokoto.
Rahotanni sun ce sojojin na kan hanyarsu ta amsa kiran gaggawa ne bayan wani hari da ‘yan bindiga suka kai wa al’ummar yankin a safiyar ranar Asabar.
Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun shiga ƙauyen ne tsakanin ƙarfe 12:30 na dare zuwa 3:00 na safe, inda suka riƙa harbe-harbe, lamarin da ya sa jama’a suka nemi taimakon jami’an tsaro.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya yi zargin cewa maharan sun dasa bam ɗin ne a kan hanyar Isa zuwa Bargaja kafin isowar sojojin.
A wani bidiyo da aka ce Turji ya fitar bayan harin, ya nuna farin cikinsa kan mutuwar wasu daga cikin waɗanda ya kira maƙiyansa.
A cewarsa, Allah ya ba su nasara a kan mutanen da yake zargi da kwace musu dabbobi da kuma kashe mutanensu a wasu yankuna da suka haɗa da Isa, Sabon Birni da wasu sassan jihohin Sokoto da Zamfara.
Turji ya kuma yi ikirarin cewa sun kashe wasu daga cikin waɗanda ke yaƙar su tare da ƙwato dabbobin da aka karɓe musu.
Sai dai jaridar Daily Trust ta ce ba ta samu damar tabbatar da gaskiyar waɗannan ikirarai daga wata majiya mai zaman kanta ba har zuwa lokacin haɗa rahoton.
A wani ci gaba kuma, an samu ƙarin fargaba kan tsaro bayan wani mai fafutukar tabbatar da adalci da kyakkyawan shugabanci a jihar Sokoto, Basharu Altine Guyawa Isa, ya yi zargin cewa Turji na ci gaba da ƙarfafa mayaƙansa tare da samun sabbin makamai a yankunan kan iyakar Sokoto da Zamfara.
A wani saƙo da ya wallafa a Facebook, Basharu ya yi zargin cewa wasu daga cikin mayaƙan Turji na gudanar da atisayen amfani da makamai a yankunan Bingabale Kudu, Bafarawa ta Gabas da Bargaja.
Ya kuma yi ikirarin cewa wasu sabbin mayaƙa masu alaƙa da ƙungiyar Boko Haram sun isa yankin domin horas da mayaƙan Turji dabarun yaƙi da amfani da makamai.
Basharu ya ƙara da cewa bincikensa ya nuna cewa Turji ya mallaki wasu sabbin kayan aikin yaƙi, ciki har da na’urar hangen dare, tare da zargin cewa wasu shugabannin ‘yan bindiga sun taimaka wajen samar da makaman.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ba ta yi wani martani ba kan waɗannan zarge-zarge, duk da ƙoƙarin da aka yi na tuntubar kakakinta, DSP Ahmad Rufai.
