KNGH/KYAUTA
Gwamnan Kano Abba Kabir Yuisf ya amince da baiwa SA PA SR da SSR da suke taimaka masa a fannin siyasa sama da filaye 300 domin su gina gidaje, tare da da baiwa kowannensu gudunmawar naira dubu ɗari.
Gwamnan ya basu kyautar ne a wajen wani taro da gwamnan ya kira wanda ya kunshi dukkan masu taimaka masa wajen gudanar da Mulki daga kowane fanni.
Gwamnan ya ce bayar da kyautar filayen zai taimaka musu wajen mallakar muhalli tare da kara musu kaimi wajen sadaukar da kai a kan dukkanin sha’anin da ya shafi taimakawa gwamnan wajen gudanar da Mulki.
Da yake jawabi a wajen taron, Kakakin Majalisar dokokin Jihar Kano, Ismail Falgore, ya ce jam’iyyar APC ba ta da wani abin kunya wajen tallata nasarorin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a jihar Kano, a dan haka zasu yi tallan sa iyakcin iyawar su har sai ya kai ga nasara a zabe mai zuwa.
Shi ma Shugaban jam’iyyar APC na Kano, Umar Haruna Doguwa, ya bayyana cewa jam’iyyar ta shirya tsaf domin tunkarar zaɓen 2027, yana mai nuna kwarin gwiwar cewa APC za ta yi nasara a dukkan matakai.
KUK
