Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta sake jaddada umarninta na a ci gaba da kiyaye halin da ake ciki kan wani rikicin fili No 17 layin Bashir Magashi a kan titin UDB dake Hotoro a karamar hukumar Nasarawa, tare da gargadin wani babban jami’in rundunar ‘yan sanda, ACP Babagana dake shiyya ta daya a Kano, kan zargin kin bin umarnin kotu. Hukuncin ya biyo bayan karar da Alkasim Musa da Mahaboob Mohammed Radman suka shigar a gaban kotun kan takaddamar mallakar filin.
Wannan ya biyo korafin da Lauyan masu ƙara Barrister Bashir Yusif Muhammad ya shigar gaban kotu a ranar 22 ga wata Yuli 2026, inda ya zargi ACP Babagana da raina kotu, bayan ya tura jami’an wurin da ake ta kaddamar akai, duk kuwa da umarnin kotu na cewa kowa ya dakata
Mai shari’a Simon A. Amobeda ya ce kotun ta gamsu da hujjojin da aka gabatar cewa ACP Babagana ya yi watsi da umarnin kotun duk da cewa an ba shi takardar gargadi ta Form 48. Kotun ta ce an kuma zarge shi da ci gaba da aikata abubuwan da ka iya haddasa tashin hankali da kuma kawo cikas ga gudanar da adalci. A cewar mai shari’ar, “Kotun ta gamsu cewa wanda ake kara na biyar ya yi watsi da umarnin wannan kotu da gangan kuma cikin sani.”
Saboda haka, kotun ta sake tabbatar da umarninta na ranar 20 ga Yulin 2026, inda ta hana dukkan bangarorin da wakilansu shiga filin, lalata shi ko kuma tsoma baki ta kowace hanya har sai an yanke hukunci kan karar. Ta kuma gargadi ACP Babagana da ya daina duk wani abu da zai saba wa umarnin kotu tare da bin dukkan umarnin da aka bayar.
Haka kuma kotun ta umurci babban Sufeton ‘Yan Sanda da ya tabbatar an aiwatar da umarnin kotun, tare da daukar matakin ladabtarwa kan ACP Babagana, Kotun ta kuma umarci hukumar tsaro ta Civil defens da ta karbi ragamar kula da wurin, sannan ta tabbatar an dawo da duk kayayyaki da aka sace daga gidan
Kotun ta kuma umurci Gwamnatin Jihar Kano, Kwamishinan Filaye da su dauki matakan kare filin da tabbatar da zaman lafiya.
Kotun ta kara da cewa duk wanda aka samu a wurin ba tare da izini ba yayin da umarnin ke aiki, na iya fuskantar tsarewa har sai an kammala sauraron karar.
