Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bukaci fadar shugaban ƙasa ta riƙa wallafa hotuna da bidiyo masu ɗauke da kwanan wata a kullum, domin tabbatar da cewa shugaba Bola Tinubu yana gudanar da ibadar Umara a Makka kamar yadda aka sanar.
Atiku ya yi zargin cewa akwai yiwuwar tafiyar Tinubu zuwa Umara ta kasance wata hanya ta ɓoye ainihin inda zai je, yana mai cewa bayanan sirri da yake da su sun nuna cewa Faransa ce ainihin inda shugaban zai nufa.
A sanarwar da daraktan yaɗa labarai na yaƙin neman zaɓensa, Phrank Shaibu ya fitar, Atiku ya ce akwai yiwuwar Tinubu ya ɗan tsaya a Makka kafin ya wuce Faransa.
Ya kuma yi tambayoyi kan ko tafiyar tana da alaƙa da lafiyar shugaban ƙasar da kuma rahoton neman rancen dala biliyan 20 a Faransa.
Atiku ya buƙaci fadar shugaban ƙasa ta bayyana cikakken jadawalin tafiyar Tinubu, tare da bayar da bayani kan ayyukan da zai gudanar a kowacce rana da kuma yadda ake ɗaukar nauyin tafiyar.
Ya ce idan da gaske shugaban ƙasar ya tafi Makka ne domin yi wa Najeriya addu’a, ya kamata a riƙa wallafa sabbin hotuna da bidiyo da ke nuna shi a gaban Ka’aba da kuma yayin gudanar da ibadun Umrah.
