Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta ce yau za ta tattauna kan makomar yan takarar da cire sunayensu.
Waɗanda ta cire sunayen nasu sun haɗa da Aminu Abdussalam Gwarzo da tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Pantami da Ladi Adebutu tare da sauran yan siyasar da aka cire daga jerin sunayen yan takarar zaɓen gwamnonin da za a gudanar ranar 6 ga Fabrairu, 2027.
Kwamishinan INEC na ƙasa, Mohammed Haruna, ne ya bayyana hakan a wata hira ta musamman da jaridar The Punch jiya Laraba, inda ya ce hukumar za ta tattauna batun a taronta na yau Alhamis.
INEC ta cire sunan Aminu Gwarzo, ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NDC da Pantami da ke neman kujerar gwamnan jihar Gombe a PDP, yayin da Adebutu ke takarar gwamnan jihar Ogun a jam’iyyar ta PDP sai kuma Danjuma Laah na jihar Kaduna da sauran yan takara.
INEC ta bayyana cewa an cire sunayen yan takarar ne saboda jam’iyyunsu sun kasa gabatar da rajistar mambobinsu a cikin wa’adin da doka ta tanada.
Matakin ya biyo bayan hukuncin Kotun Ƙoli na ranar 24 ga Satumba, 2026, wanda ya tabbatar da ingancin wasu sassan Dokar Zaɓe ta 2026 da ke buƙatar jam’iyyun siyasa su gabatar da rajistar mambobinsu ga INEC kafin gudanar da sahihin zaɓen fidda gwani da sauran tarukan jam’iyya.
INEC ta ce wa’adin gabatar da rajistar mambobin ya kasance daga 21 ga Afrilu zuwa 10 ga Mayu, 2026, kuma jam’iyyun da ba su cika wannan sharadi ba ba su cancanci tsayar da yan takara ba.
Sai dai jam’iyyun da abin ya shafa sun dage cewa sun bi dukkan ƙa’idojin doka, tare da neman INEC ta gyara abin da suka kira kuskuren cire sunayen yan takararsu.
Yanzu haka dai ana jiran tattaunawar hukumar a taronta na yau Alhamis domin sanin matakin da za ta ɗauka kan ƙorafe-ƙorafen.
