Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa APC ya bayyana mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima a matsayin abokin takarar shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ne ya sanar da hakan ta shafinsa na X, inda ya ce jam’iyyar ta karɓi takardun tsayawa takara na Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Yilwatda ya bayyana wannan a matsayin wani muhimmin mataki da ke nuna ƙudurin jam’iyyar na ci gaba da aiwatar da manufar Renewed Hope Agenda, tare da ƙarfafa ci gaban da gwamnati ke cewa tana samu a ƙasar nan.
Wannan mataki ya kawo ƙarshen watanni na rade-radin cewa Shugaba Tinubu na iya sauya Shettima da wani Kirista daga Arewa a matsayin abokin takararsa a zaɓen 2027.
Ya ƙara da cewa mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa da sauran lamurra, Ibrahim Masari, ne ya gabatar da takardun a madadin Shugaba Tinubu a wani taro da aka gudanar a Abuja.
Yilwatda ya ce gabatar da takardun na nuna cikakkiyar amincewar jam’iyyar da shugabancin Tinubu da Shettima, yayin da suke shirin neman wa’adin mulki na biyu daga yan Najeriya.
