Rundunar Sojin ƙasar nan ta ƙaddamar da sabbin rundunoni uku a Birnin Kebbi, Yawuri da Ka’oje domin ƙarfafa ayyukan tsaro a Jihar Kebbi.
Wannan na cikin sanarwar da Muƙaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Runduna ta 8, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, ya fitar a ranar Litinin.
Rundunonin sun haɗa da Runduna ta 28 mai sulke a Birnin Kebbi, Bataliya ta 281 ta tankokin yaƙi a Yauri da Runduna ta 381 ta manyan makaman atilari a Ka’oje.
A nata ɓangaren, Gwamnatin Jihar Kebbi ta yi maraba da matakin, inda ta bayyana cewa kafa rundunonin zai taimaka wajen inganta ayyukan tsaro.
